17 Satumba 2025 - 20:56
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Katse Internet A Wani Babban Yankin Gaza

Hukumar sadarwar Falasdinu ta sanar da katse ayyukan intanet da na wayar tarho a birnin Gaza da arewacin zirin Gaza sakamakon hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai kan manyan hanyoyin sadarwar.

A wani ɓangare kuma sojojin Isra'ila sun biyan kudi da bada filaye, lada wadanda suka kawo bayanan sirri a Gaza kamar yadda Jaridar Haaretz ta bayar da rahoton cewa, sojojin Isra'ila sun fara daukar sojojin haya a yankin zirin Gaza domin fuskantar gwagwarmaya.

Wadannan da ake bawa makamai da kudade suna gudanar da ayyuka ne ga sojojin mamaya domin musanyar bayanai.

Daya daga cikin wadannan sojojin hayan dai na alaka da Abu Shabab, wadanda ke hadin gwiwar aiki tare da jami'an tsaron Isra'ila Shin Bet da sojojinta kuma suka samu izinin daukar makamai daga gwamnatin kasar.

Waɗannan ƴan bindigar suna samun riba mai yawa ta hanyar wawashe kayan agaji kuma suna aiki kai tsaye ƙarƙashin kulawar Shin Bet (ma'aikatar tsaron cikin gida ta Isra'ila) da kuma sojojin gwamnatin.

Your Comment

You are replying to: .
captcha